Hakkin mallakar hoto AFP Image caption Masana kimiyya a Beijing na gudanar da daya daga cikin gwamman bincike domin samo riga-kafin korona

Sama da dala biliyan 8 aka tara domin taimakawa wajen samar da allurar riga-kafin cutar korona da kuma bincike don samar da maganin cutar.

Kasashe 40 da kuma masu ba da taimako sun shiga cikin taron da aka yi ta intanet wanda Hukumar Tarayyar Turai ta jagoranta don samar da riga-kafin cutar.

Shugabar hukumar Ursula von der Leyen ta ce kudin za su taimaka wajen samar da wani hadin kai a duniya wanda ba a taba samu ba.

Ta ce ya nuna karfin hadin kai da kuma tausayawa masu rauni, amma ta yi gargadin akwai bukatu masu yawa da za su zo nan gaba.

  • Muna kukan rashin Shugaba Umar 'Yar Adua - Jonathan
  • Sarakuna masu daraja ta Ɗaya da suka mutu a Najeriya
  • Annobar ta ninka fiye da sau 2 cikin mako a arewacin Najeriya

Ya zuma yanzu sama da kasashe 30 da kuma Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin ba da agaji da cibiyoyin bincike ne suka ba da na su tallafin.

Cikin wadanda suka ba da agajin har da mawakiyar nan ta Amurka Madonna, wadda ta ba da dala miliyan 1.1, in ji Misis von der Leyen, wacce kuma ita ce ta kafa gidauniyar Bruassels a ranar Juma'a.

Kungiyar tarayyar Turai ta bayar da dala biliyan 1 don samar da riga-kafin. Norway ma ta ba da kwatankwacin abin da Tarayyar Turai ta bayar, Faransa ta ba da yuro miliyan 500, kamar yadda Saudiyya da Jamus suka bayar. Japan ta ba da sama da dala miliyan 800.

Amurka da Rasha ba su halarci taron ba. China, inda a can ne aka samu bullar cutar a watan Disambar bara, ta samu wakilcin jakadanta na kungiyar Turai.

Kungiyar Turai ta ce za a yi amfani da dala biliyan 4.4 da aka tara wajen samar da allaurar riga-kafi, dala biliyan 2 kuma wajen bincike kan maganin, dala biliyan 1 kuma wajen samar da kayan gwaji.

Yayin bayaninta na bude taron, Misis von der Leyen ta ce dole ne kowa ya ba da nasa tallafin kudin, "a wani fadi-tashi da duniya ke fuskanta".

"Na yi amannar ranar 4 ga watan Mayu za ta samar da wani gagarumin ci gaba a yakin da ake da korona, saboda a yau duniya ta hade wuri guda, ta ce.

Abokan tafiyar na da yawa, kuma abu daya ake son cimmawa shi ne kawo karshen cutar."

Firaiministan Burtaniya Boris Johnson wanda shi ma na cikin wadanda suka jagorancin taron, ya ce "Yanayin yadda muka hada kai tare wajen aiki da kwarewar mu, yanayin yadda masana kimiyya za su samu nasara cikin gaggawa" wajen samar da riga-kafin.

Mista Johnson, wanda ya kwashe kwanaki uku a sashen kulawa ta musamman saboda cutar, ya tabbatar da Burtaniya ta ba da fan miliyan 388 na allaurar da kayan gwajin da kuma maganin cutar a yayin taron.

Bayan Hukumar Tarayyar Turai, kasashen Burtaniya da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da Norway da Saudiyya suna cikin wadanda suka jagoranci taron.

Hakkin mallakar hoto Getty Images Image caption Emmanuel Macron da Angela Merkel, a hton da aka dauka bara, suna cikin shugabannin kasashen duniya da suka sanya hannu kan wasikar

Firaiministan Italiya Giuseppe Conte, Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na cikin wadanda suka rattaba hannu kan wannan taimako.

A farkon wasikar da aka wallafa a karshen mako a jaridu, shugabannin sun ce "kudin za su taimaka wajen samar da wani hadin kai a duniya wanda ba a taba samu ba tsakanin masana kimiyya da mahukunta da masu masana'antu da gwamnatoci da kungiyoyin duniya da gidauniyoyi da kuma kwararu kan kiwon lafiya".

"Idon za mu iya samar da riga-kafin ga duniya baki daya, wannan zai zama wani abu mai kyau da aka yi wa al'umma a karnin na 21," suka kara da cewa.

A lokaci guda kuma, mahalarta taron sun nuna goyon bayansu ga Hukumar Lafiya ta Duniya kan yadda Amurka ke sukarta saboda gaza tafiyar da cutar yadda ya kamata.

Majalaisar Dinkin Duniya ta ce za a iya dawowa rayuwa kamar da, idan an samu allarar riga-kafin amma.

Gwamman masu bincike ne ke aikin binciken riga-kafin wannan cuta yanzu a fadin duniya.

Duk da taimakon kudin da aka samu, zai dauki lokaci mai tsawo kan a san wanne magani ne zai aiki kuma da ingancinsa.

Mafi yawan masana na ganin zai kai tsakiyar shekarar 2021, ko kuma wata 12 zuwa 18 kan a samu rigakafin wannan cuta.