Hakkin mallakar hoto Misbahu M Ahmad Image caption Sanusi Oscar (na biyu daga hagu) mai shirya fina-finai ne a Kannywood

Wata kotun majistire a jihar Kano ta bayar da belin darakta Sanusi Oscar a masana'antar Kannywood bayan hukumar tace fina-finai ta gurfanar da shi a gabanta bisa zargin saba kai'dar aiki.

Hukumar ta gurfanar da Oscar a gaban kotun ne saboda ya "saba ka'idojin gudanar da sana'arsa a Kano, inda ya saki wata waka wadda akwai badala a ciki", kamar yadda shugaban hukumar Isma'ila Na'abba Afakallahu ya shaida wa BBC.

Alkali Aminu Fagge na kotun majistire mai lamba 34 da ke Rijiyar Zaki ne ya jagoranci zaman kotun, inda ya bayar da belin Oscar bisa sharudda.

Sharuddan sun hada da cewa wajibi ne mutum biyu su tsaya masa kuma daya daga cikinsu ya zama dan uwansa na jini, tare da haramcin magana da kowacce irin kafar yada labarai.

Kotun har wa yau, ta sanya ranar 10 ga watan Satumba domin zamanta na gaba.

  • Adam A. Zango ya ce ya fita daga Kannywood
  • Hukuncin kotun Birtaniya 'zai wa Najeriya illa'

Tuni abokan aikinsa suka fara mayar da martani game da sakin nasa.

Misbahu M. Ahmad ya wallafa bidiyo a shafinsa na Instagram yana maraba da hukuncin kotun.

Abin da ya biyo bayan kama Oscar
Hakkin mallakar hoto Sanusi Oscar

Akasarin 'yan fim din sun rabu gida biyu - masu goyon bayan jam'iyyar APC mai mulki da kuma bangaren hamayya na PDP (wato Kwankwasiyya a Kano), kuma siyasa kan fito fili a wasu ayyukansu.

Tun bayan kamun nasa ne manyan taurari a masana'antar suka rika mayar da zafafan martani, inda Adam Zango ya ce "ya fice daga kannywood" sannan shi ma Mustapha Nabraska ya ce ya "daina wasan Hausa har sai an sako abokin aikin nasu".

Tauraro fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango, yana daya daga cikin mutanen da suka fara bayyana bacin ransu dangane da batun.

Abin da ya sa shi fita daga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Jarumi Mustapha Nabraska shi ma ya bayyana cewa ya daina wasan Hausa saboda kama abokin aikinsu.

Sai dai Sani Danja ya bukaci a warware matsalar ta hanyar maslaha, "ba tare da cin zarafin mutum ba," kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram.

Ya ce kama Oscar "ba daidai ba ne," hakazalika ya bukaci duka 'yan Kannywood da su dauki kansu a matsayin 'yan uwan juna kuma su kasance tsintsiya madaurinki daya.

Ita ma shahararriyar jarumar Kate Henshaw wacce take fitowa a fina-finan kudancin Najeriya wato Nollywood, ta yi Allah-wadai da kama daraktan, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram.